By: Admin
KADUNA, North-West Nigeria – Hukumar Bunkasa Rayuwar Jama’a ta Kasa, National Social Investment Programme Agency, N-SIPA, ta sako tallafin naira 24, 781,525,000 ga masu karamin karfi a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Bayanin farfado da shirin tallafawa al’ummar yana kunshe ne a cikin wata takardar bayani ga manema labarai mai dauke da sa hannun shugabazn NSIPA, Farfesa Badamasi Lawal a ranar Alhamis 26 ga Satumbar 2024.
Takardar ta bayyana cewa an tura kudin ga mutane 991,261 kuma kowannensu ya amfana da naira 25,000.
Farfesa Badamasi Lawal ya bayyana matakin a matsayin cika alkawarin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunkasa rayuwar ‘yan Nijeriya, wanda ake yi wa lakabi da Renewed Hope Agenda da Turanci.
Idan za a iya tunawa, Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da wannan shiri sakamakon zargin almundahar kudi da aka yi zargin wasu manyan ma’aikatan Ma’aikatar Tallafawa Al’umma da aikatawa, wadda ta yi sanadin korar wasu daga aiki.
Farfesa Badamasi ya kuma bayyana cewa hukumar ta saki naira 3, 825,950,000 ga mabukata 153,038 a watan Agusta, 2024.
Ana gudanar da wannan shiri ne domin tallafawa masu karamin karfi a birane da yankunan karkara domin ba su tagomashin rayuwa